Gwamnatin Jihar Edo ta ba da umarnin rufe makarantun sakandare 3 a Karamar Hukumar Akoko-Edo nan take sakamakon bayanan sirri da ke nuna an tsara kai harin sace dalibai.
Makarantun da lamarin ya shafa sun hada da Ososo Grammar School, Ososo Comprehensive High School da Makeke Secondary School.
Umarnin ya fito ne a cikin wata takardar sanarwa mai kwanan wata 9 ga Yuni wadda Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi na jihar Mr Enodolomwanyi Otamere ya sanya wa hannu.
An yanke shawarar ne bayan shawarar tsaro daga hukumomin da abin ya shafa da suka, inda suka yi gargadin cewa akwai barazana ta gaske ga tsaron dalibai, malamai da mazauna wasu sassan Akoko-Edo.
“Ma’aikatar Ilimi ta samu bayanan sirri da shawarwari daga hukumomin tsaron game da barazana ta gaske dangane da tsaron dalibai, ma’aikata, da al’ummomin makaranta a wasu sassan Karamar Hukumar Akoko Edo,” in ji Otamere.
Ya ce an dakatar da dukkan ayyukan karatu da sauran ayyuka a makarantun da abin ya shafa har sai komai ya daidaita matsayin matakin kariya domin kare rayuka da dukiyoyi.
Rufe makarantun ya zo ne bayan rahoton sirri na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), wanda ya bankado wani zargi shiri da ‘yan bindiga ke yin na sace daliban makaranta a yankin Edo ta Arewa.
A cewar rahoton, jami’an tsaro sun datsi wata hira tsakanin ‘yan bindiga biyu, wadanda ake zargin suna tattauna karkatar da hankalinsu zuwa daliban makaranta bayan kokarin sace masu kudi da suka yi bai samar da kudin da suka yi tsammani ba.
Rahoton ya kara bayyana cewa an kama wani mutum dan shekara 25 a ranar 4 ga Yuni, wanda ake zargin yana leken asiri a kusa da Makeke Secondary School, lamarin da ya haifar da damuwa cewa shirin kai harin ya riga ya fara.
Bayan lamarin, hukumomin tsaro sun ba da shawarar a kara matakan kariya a makarantu, tura karin jami’ai, karfafa hadin gwiwa da kungiyoyin ‘yan banga na gari da masu farauta, tare da kara yawan sintiri a al’ummomin da ke cikin hadari.
Duk da rufe makarantun, gwamnati ta ce daliban da ke rubuta Jarabawar Kasashen Yammacin Afirka (WAEC) a yanzu za su ci gaba da zama don rubutu jarrabawar karkashin tsarin tsaro mai karfi.
“Za a bai wa daliban da ke rubuta Jarabawar Kasashen Yammacin Afirka (WAEC) damar shiga domin yin jarrabawarsu karkashin tsarin tsaro mai tsauri da kulawa kamar yadda hukumomin tsaron da suka dace da masu ruwa da tsaki a al’umma za su tanadar,” in ji Otamere.
Ya umarci hukumomin makaranta su tabbatar sun sallami dalibai zuwa ga iyayensu da masu kula da su cikin tsari, su kiyaye kayan makaranta, sannan su ci gaba da sanar da jami’an gwamnati da hukumomin tsaro.
Gwamnati ta kuma roki mazauna yankin da iyaye da su kwantar da hankalinsu tare da hadi gwiwa da hukumomin tsaro yayin da ake kokarin kawar da barazanar dawo da ayyukan karatu na yau da kullum.












































