Binciken Kudi: Majalisar Dattawa ta ba da umarnin kamo tsohon shugaban kamfanin mai na kasa Mele Kyari

Mele Kyari

Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Asusun Jama’a ya ba da umarnin fitar da takardar kamawa da za ta tilasta wa tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari bayyana a gabansa don amsa tambaya kan gudanar da harkokin kudi da warware bayanan da suka shafi Naira Tiriliyan 210 da ke cikin kididdigar kudin kamfanin daga shekarar 2017 zuwa 2023.

Kwamitin ya yanke shawarar ne bayan Kyari ya ki amsa gayyatar da aka yi masa sau 9 a jere, duk da cewa shi ne babban jigo a binciken da ake yi kan batutuwan da rahotannin Binciken Asusun Tarayya ya yi daga lokacin da ake magana.

‘Yan majalisa sun dage cewa dole tsohon shugaban na NNPCL ya bayyana a gaban kwamitin domin yin bayani kan tambayayin da suke cikin bayanan kudi da aka bayyana.

Sanata Victor Umeh ya bukaci kwamitin ta fitar da takardar kamu ga Kyari, yana mai cewa ya yi watsi da gayyatar da kwamitin ya yi masa, saboda kwamitin bazai ci gaba da jira na har abada.

Sanata Adams Oshiomhole ne ya gabatar da kudirin fitar da takardar kama Kyari, inda ya ce duk wani kokari da kwamitin ya yi na ganin Kyari ya halarci tattaunawar ta ci tura.

Yawancin mambobi sun goyi bayan kudirin kuma an amince da shi da murya, lamarin da ya bada damar fitar da takardar kamun.

Yayin zaman, Sanata Tony Nwoye ya roki kwamitin da ya yi hakuri, inda ya bayyana cewa ya yi magana da Kyari kusan mako guda da ya gabata kuma tsohon shugaban NNPCL ya shaida masa zai bayyana a gaban kwamitin.

Nwoye ya kara sanar da kwamitin cewa ya samu bayani cewa Kyari na karbar magani a Jamus a yanzu.

Shigar Nwoye ta haifar da muhawara mai zafi daga wasu ‘yan majalisa, ciki har da Sanata Onyekachi Nwebonyi, wanda ya ce kin amsa gayyatar da Kyari ya yi, ya nuna rashin mutunta Majalisar Dattawa da ‘yan Najeriya.

Shugaban Kwamitin, Sanata Ibrahim Dankwambo, ya lura cewa kwamitin ya bai wa Kyari da sauran tsofaffin jami’an NNPCL dama mai yawa na su bayyana don yin bayana kan abin da ke cikin kididdigar kudin, yana mai jaddada cewa kwamitin yana gudanar da aikinsa da kundin tsarin mulki ya bashi na tabbatar da gaskiya wajen sarrafa kudaden jama’a.

Duk da rashin halartar Kyari, kwamitin ya ci gaba da zama kuma ya karbi shaida daga mambobi 2 na tsohon jagorancin NNPCL, tsohon Babban Jami’in Kudi, Umar Ajiya, da tsohon Babban Jami’in Zuba Jari na Hako Man Fetur, Bala Wunti.

Kwamitin ya sake jaddada kudurin sa na binciken kudaden hukumomin gwamnati da tabbatar da gaskiya da lissafin yadda aka sarrafa albarkatun jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here