IPMAN ta yi barazanar shiga yajin aiki a Najeriya kan bashin Naira Biliyan 100 da ta ke bin gwamnati

IPMAN logo

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta (IPMAN) ta bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kayyade farashin man fetur da ta biya su bashin da suke bin ta na Naira biliyan 100.

Kungiyar ta yi barazanar janye ayyukanta idan ba a biya su kudaden ba kafin wa’adin.

Wannan matakin ya biyo bayan gazawar da NMDPRA ta yi na biyan basussukan, duk da alkawuran da ta yi kwanaki 40 da suka gabata a gaban mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Karin karatu: “Karancin Man fetur zai dauki a kalla makonni biyu” – IPMAN

Cikin alkawarin ƙungiyar ta ce rashin warware bashin, zai iya haifar da karancin Motoci a fadin kasar baki daya.

Shugaban kungiyar IPMAN Yahaya Alhasan ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin inda ya nuna takaicinsa kan gazawar NMDPRA na cika alkawarin da aka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here