Ba mu san yadda aka yi Tinubu ya nada Yusuf Ata minista ba” – Abdullahi Abbas

Abdullahi Abbas APC

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya ce nadin Yusuf Abdullahi Atta a matsayin minista da shugaba Bola Tinubu ya yi, abin mamaki ne domin shi ba dan jam’iyya ba ne.

Abbas ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC wanda SolaceBase ta nazarta a lokacin da yake mayar da martani kan kalaman da karamin ministan gidaje da raya birane, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata ya yi a kwanakin baya, inda ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar.

Ministan ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC idan har aka sake zaben shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar a karo na hudu.

Abbas ya shaida wa BBC cewa Yusuf Ata “ba dan jam’iyya ba ne,” kuma sun yi mamakin dalilan da suka sa aka nada shi minista.

Abbas ya ce burinsa shi ne ya zama gwamnan jihar, ba wai ya ci gaba da zama shugaban jam’iyyar ba.

SolaceBase ta ruwaito cewa a halin yanzu, kalaman da ministan ya yi a wani faifan bidiyo a karshen makon da ya gabata ya kara fallasa dambarwar siyasar APC a Kano.

Har ila yau, a wata sanarwa da mai bada shawara na musamman kan harkokin kafafen yada labarai na ministan Adamu Aminu ya fitar, ta ce ministan ya jaddada bukatar shugabannin jam’iyyar su guji furta kalaman batanci ga Allah Madaukakin Sarki.

Labari mai alaƙa: Rikici ya barke a APC yayin da Ganduje, da minista suke jayayya kan amincewa da shugabancin jam’iyyar na jiha

Ata ya alakanta kalaman “Koda Tsiya, Koda Tsiya-Tsiya” da shugabancin jam’iyyar APC a jihar Kano ya furta yana mai bayyana hakan a matsayin rashin mutunta girman Allah.

Ya yi gargadin cewa irin wadannan kalamai na iya haifar da mummunan sakamako da suka hada da fushin Allah da kuma shan kaye a zabe.

Ministan ya yi kira ga shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, da ya hada kan jam’iyyar tare da samar da tsari ga mambobinta.

Ya kuma jaddada cewa ya zama wajibi shugabannin jam’iyyar su ladabtar da duk wani dan jam’iyya da ya yi rashin biyayya ga Allah, tare da tabbatar da cewa ayyukan jam’iyyar sun yi daidai da kimar mabiya addininta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here