Gwamnonin Kudu maso Yamma ba su da ikon dakatar da ayyukan Shari’a – Alkali

Sharia 750x430

Wani Qadi na Kotun Daukaka Kara ta Shari’a a Jihar Kwara, Mai Shari’a Abdurraheem Sayi, ya yi watsi da korafe-korafen da aka yi wa kwamitin sulhu na Shari’a a yankin Kudu maso Yamma a matsayin mai nuna kyama ga Musulunci.

Mai shari’a Sayi ya ce ba a bukatar amincewar hukumomin jiha ko sarakunan gargajiya don kafa kwamitin sulhu na Shari’a a yankin Kudu maso Yamma.

A cewarsa, adawar “ba ta da tushe a shari’a” kuma abin kunya ne ga masu tunani.

Karin karatu: Kotu ta ɗage shari’ar Nnamdi Kanu har sai yadda hali ya yi

Alkalin ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da lakca ta kafin azumin Ramadan a Jami’ar Legas karo na 30, inda ya yi jawabi a kan “Shari’ah a Kudu maso Yammacin Najeriya.”

Mai shari’a Sayi ya ce, “Babu wani rudani a kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma Musulmin Kudu maso Yamma ba sa bukatar izini ko amincewar wasu kungiyoyin addini ko sarakunan gargajiya don gudanar da ayyukan Shari’a.

Ya bayyana cewa dokar sasantawa ta 2023 ta ba wa ‘yan kasa masu zaman kansu damar kafa kwamitin sasantawa tare da ba su ikon tantance tsarin doka da ke tafiyar da irin wadannan bangarorin.

Ya ci gaba da cewa, bai kamata a hana musulman Legas, Osun da Ogun tsarin shari’a kamar kotunan Shari’a ba, inda za a iya magance al’amuransu na kashin kansu da na iyali.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here