USAID ta umurci ma’aikata 1,600 da su ci gaba da hutun dakatarwar da ta yi musu

USAID USAID 750x430

Hukumar raya kasashe ta Amurka USAID, ranar Lahadi da karfe 11:59 na dare ta sanya umarci kimanin ma’aikata 1,600 a duk duniya da su ci gaba da hutun dakatarwar da ta yi musu.

Hukumar ta sanar da hutun ne a cikin wata sanarwa mai taken “Sanarwar izinin Gudanarwa”, ta kafar internet na hukumar.

Ya kara da cewa, “A halin da ake ciki, USAID ta fara aiwatar da wani matakin rage karfinta da zai shafi kusan ma’aikatan hukumar ta USAID 1,600.”

Ma’aikatan da abin ya shafa sun sami sanarwar kai tsaye, tare da cewa su ci gaba da zama har sai sun samu cikakken bayani kan matakai na gaba game da matsayin aikinsu.

Karanta: Janyewar hukumar USAID na daɗa haifar da bazuwar cutar HIV a Bauchi

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, an dorawa wasu zababbun ma’aikatan alhakin ci gaba da gudanar da ayyuka wadanda shugabannin hukumar suka zaba, ana sa ran za su ci gaba da kasancewa a cikin ayyukansu duk da sauye-sauyen da aka samu.

Tasirin waɗannan sauye-sauye ya bayyana musamman ga ma’aikatan USAID na ketare. Sai dai hukumar ta yi alkawarin tabbatar da tsaron lafiyarsu.

Har ila yau, an shawarci ma’aikatan da ba sa amfani da tsarin na USAID da su duba USAID.gov don samun sabbin bayanai, kamar yadda jami’an hukumar suka yi alƙawarin ci gaba da sanarwa ta hanyoyin sadarwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here