Kamaru ta zama kasar farko da ta kaddamar da gangamin rigakafin cizon sauro

maleriya, sauro, cizo, kamaru
Yau Litinin Kamaru ta kaddamar da aikin gangamin rigakafin zazzabin cizon sauro, matakin da ya mayar da ita kasar farko da ta jagoranci wannan aiki a wani...

Yau Litinin Kamaru ta kaddamar da aikin gangamin rigakafin zazzabin cizon sauro, matakin da ya mayar da ita kasar farko da ta jagoranci wannan aiki a wani yunkuri na yakar cutar wadda sauro ke yadawa.

Gangamin na Kamaru na zuwa ne bayan gwajin alluran rigakafin cutar a kasashen Ghana da Kenya, wanda masana suka tabbatar da tasirin rigakafin wajen iya kange yara daga kamuwa da cutar.

Karanta wannan: Majalisar Dattawa za ta gayyaci Wike kan karuwar satar mutane – Kingibe

Bayan tababar kusan shekaru 40 wajen tantance sahihancin rigakafin cutar ta Maleriya, WHO ta amince da allurer rigakafin na zazzabin cizon da za ta zama cikakkiyar kariya ga illar da cutar ke yi musamman a nahiyar Afrika.

Alkaluma sun nuna yadda cutar ta Malaria ko kuma zazzabin cizon sauro ke kisan yara ‘yan kasa da shekaru 5 kusan rabin miliyan duk shekara a Afrika.

A cewar hadakar da ke aikin samar da rigakafin cutuka, yanzu haka kasashe 19 ne za su fara amfana da rigakafin a shekarar nan kadai.

Karanta wannan: Jami’an tsaro sun kubutar da ‘yan uwan Nabiha da aka yi garkuwa da su

Akalla yara miliyan 6 da dubu 600 ake saran zu amfana da rigakafin zazzabin na cizon sauro cikin 2024 zuwa 2025 a kasashen da zuwa yanzu suka yi rijista don samun rigakafin.

Babban daraktan yaki da cutuka na hukumar dakile yaduwar cutuka ta Afrika CDC Mohammed Abdul’aziz ya ce lokaci ne da hukumar ta jima ta na dako lura da muhimmancin rigakafin ga nahiyar wadda ta fi kowacce rasa rayuka sakamakon cutar ta Maleriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here