Gwamnatin tarayya ta janye dukar hana tura yan bautar kasa bankuna da sauran ma’aikatu

nysc 1

Gwamnatin tarayya ta soke duk wani takunkumin da ta kakabawa masu yi wa kasa hidima na kasa (NYSC), wanda hakan ya share fagen tura yan bautar kasar zuwa bankuna da kamfanonin mai na kasa.

Sabon umarnin zai fara aiki ne daga kan yan Batch ‘C Orientation Course na shekarar 2024, kamar yadda wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 18 ga watan Nuwamba, 2024, daga ministan raya matasa, Kwamared Ayodele Olawande.

Canjin manufofin, a cewar Olawande, wani bangare ne na dabarun shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na yaki da karuwar rashin aikin yi ga matasa ta hanyar tabbatar da hukumomin gwamnati sun yi daidai da manufofin gwamnatinsa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here