Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Dutse a jihar Jigawa ta wanke tareda sallamar Sanata Ibrahim Saminu Turaki daga zargin almundahanar Naira Miliyan Dubu 36 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta zartas a kansa.
Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa Saminu Turaki da wasu kamfanoni 3 sun gurfana a gaban kotu tun a ranar 4 ga watan Mayun 2007 kan karar da kwamishinan dake yaki da badakalar tattalin arzikin kasa zagon kasa ya shigar kan tuhume-tuhume 33.
Hukumar ta EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban mai shari’a Binta Murtala Nyako ta babbar kotun birnin tarayya a ranar 13 ga watan Yuli, 2007, bisa tuhume-tuhume 33.
A shekarar 2011 kuma aka mayar da shari’ar zuwa babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Dutse bayan da tsohon gwamnan ya kalubalanci hurumin sashin kotun na babban birnin tarayya Abuja.
Sabon alkalin kotun, Mai shari’a Hassan Dikko da aka sake nadawa domin jan ragamar shari’ar da mai shari’a S. Yahuza ke gudanarwa a baya kafin ya yi ritaya a farkon watan Disamba.
Alkalin kotun Mai shari’a Hassan Dikko, wanda ya yanke hukuncin, ya yi watsi da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa tareda sallamar sa saboda rashin gamsuwa Kan abinda ake tuhumar su akai.
Kotun ta kuma ba da umarnin a ba shi takardun shedar tafiye-tafiyen wanda ake tuhuma na 1 wato Saminu Turaki ba tare da bata lokaci ba.
Da yake mayar da jawabi kan hukuncin, Barista Saidu Muhammad Tudunwada daya daga cikin lauyoyin da ake kara, ya ce kotun ta gamsu da hujjojin su, inda tayi fatali tareda wanke daga manyan tuhume-tuhume 33 da ake tuhumar sa da su.
Ya kara da cewa da hukuncin an yi adalci kuma nasara ce ga kowa da kowa.













































