Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ya ce kotun daukaka kara ba wanke shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu tayi ba, face kawai sallamar sa kotun tayi.
Ministan ya bayyana hakan ne cikin wata ‘yar gajeriyar sanarwa, ta hannun mai taimaka masa kan harkokin labarai Umar Jibrilu Gwandu.
Sanarwar ta ce hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan batu guda daya ne aka sallame shi bawai wanke shi kotun tayi ba cewar bashida lefi kwata kwata.
“Ima mai bayyana wa jama’a cewa sauran batutuwan da suka gabata kafin a bayar da belin Kanu an samu ingantattun bayanai ne na abar shi ahannun beli,” in ji sanarwar.
A cewar sanarwar Gwamnatin Tarayya za ta yi la’akari da dukkan wasu matakai dasuka dace dan cigaban shariar.












































