Hukumar kula da ‘yan sanda ta sanar da dakatar da jami’an ‘yan sanda biyu da ke aiki a karkashin Abba Kyari a cikin tawagar IRT.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani, inda ya ce an dakatar da nasu ne daga ranar Litinin.
Sanarwar ta ce jami’an ‘yan sandan da aka dakatar sun hada da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Sunday Ubua da mataimakin Sufeto James Bawa.
Hakan ya biyo bayan zarginsu da hannu a wani cinikin miyagun kwayoyi da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar ke bincike.
Hakazalika, an bukaci Sufeto Janar na ‘yan sandan da ya dakatar da sufeto Simon Agrigba da sufeto John Nuhu.
Sanarwar ta kara da cewa, hukumar ta kuma umurci babban sufeton ‘yan sandan kasar da ya ba ta bayanai kan ci gaban da aka samu kan lamarin domin daukar matakin da ya dace.













































