Abdulmumin Jibrin na fuskantar kora daga hukumar FHA saboda rashin da’a

5B79B765 9748 42FB 9C25 1264A91F6DA5
5B79B765 9748 42FB 9C25 1264A91F6DA5

Hukumar Kula da Gidaje ta Tarayya (FHA), ta gayyaci Babban Daraktanta na bangaren Bincike da ci gaba, Abdulmumin Jibrin Kofa, wanda zai gurfana a gaban kwamitin bincike da aka kafa akansa bisa zargin aikata rashin da’a.

An umurci Abdulmumin da ya gurfana gaban kwamitin ladabtarwa a ranar Juma’a 18 ga Fabrairu, 2022, don bayyana dalilin da ya sa ba za a kore shi daga hukumar kula da gidaje ba.

A cikin wata wasikar gayyata da shugaban kwamitin bincike/da’a, Barr. Zubairu Salihu, mai kwanan watan Fabrairu, 15, 2022, ya bayyana cewa hukumar ta kafa kwamitin ne bayan tsohon dan majalisar wakilai (Kiru/Bebeji) ya kasa amsa takardar tuhuma da manajan darakta kuma babban jami’in gudanarwa na FHA ya aika masa.

An tattaro cewa, Abdulmumin ya shafe kwanaki 92 ba ya zuwa aiki, wanda hakan ya sabawa ka’idojin da ke jagorantar ma’aikatun gwamnati.

Solacebase ta ruwaito cewa, an nada Abdulmumin Jibrin Kofa a matsayin Darakta Janar na Bola Tinubu, Social Mobilisation Group, wanda ke aiki don tabbatar da burin Bola Tinubu na zama shugaban Najeriya a 2023.

Gayyatar da aka yi wa Abdulmumin ta yi daidai da tanadin sakin layi na 8,2,0 na Hukumar Kula da Gidaje ta Tarayya, 2008, da sashe na 030307 na dokokin ma’aikatan gwamnati (2009), kamar yadda wasikar ta karanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here