Gwamnan Kano ya miƙa ta’aziyya ga majalisar dokoki kan rasuwar ‘yan majalisa biyu

1 Members 750x430

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kaɗuwarsa matuƙa bisa rasuwar ‘yan majalisar dokokin jihar Kano guda biyu da suka rasu a rana ɗaya, abin da ya bar gwamnati da al’ummar jihar cikin jimami mai tsanani.

Wannan bayani ya fito ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce, gwamnan ya bayyana rasuwar Hon. Sarki Aliyu Daneji, mai wakiltar ƙaramar hukumar Birni kuma shugaban kwamitin majalisar kan aikin hajji, da kuma Hon. Aminu Sa’adu, mai wakiltar ƙaramar hukumar Ungoggo kuma shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar dokokin jihar Kano, a matsayin lokaci mai duhu da taba zuciya a tarihin jihar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa gwamnan ya bayyana cewa wannan ibtila’i ya jefa gwamnati da jama’ar Kano cikin alhini na bai ɗaya, yana mai jaddada cewa rasa ‘yan majalisa masu cike da ƙwazo guda biyu a cikin sa’o’i kaɗan wata masifa ce mai raɗaɗi da kalmomi ba za su iya misalta ta ba.

Karanta: Yanzu-yanzu: Ƴan majalisar dokokin Kano biyu sun rasu

Ya bayyana marigayan ‘yan majalisar a matsayin jajirtattun ma’aikatan jama’a, ‘yan siyasa masu biyayya, da kuma amintattun wakilan al’ummominsu, inda ya ce jajircewarsu wajen aiki na dokoki da wakiltar jama’a a matakin tushe ba abin shakka ba ne.

Gwamna Yusuf ya ce jihar Kano ta yi babban rashi na ‘ya’ya biyu da suka sadaukar da rayukansu wajen hidimar jama’a, yana mai cewa mutuwarsu ta bar gibi mai raɗaɗi a majalisar dokoki da kuma al’ummominsu, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan, shugabanci da mambobin majalisar dokokin jihar Kano, da kuma al’ummar ƙananan hukumomin Kano Municipal da Ungoggo.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta musu kura-kuransu, Ya lullube su da rahamarSa, Ya shigar da su Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansu da al’ummar Kano ƙarfin jure wannan babban rashi, sannan ya yi kira ga jama’a da su kasance masu haƙuri, haɗin kai da yawaita addu’a, yana mai bayyana wannan lamari a matsayin jarabawar imani da juriyar al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here