Yanzu-yanzu: Ƴan majalisar dokokin Kano biyu sun rasu

WhatsApp Image 2025 12 24 at 17.32.07 750x430

Ƴan majalisar jihar Kano guda biyu da ke kan mulki sun rasu.

‘Yan majalisar sun hada da Aminu Sa’adu, wanda ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Ungoggo, da Sarki Aliyu Daneji, wanda ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Birni.

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar a wani rubutu da ya wallafa a shafin sada zumunta a ranar Laraba.

Ya ce, an samu labarin cewa Aminu Sa’adu ya kamu da rashin lafiya cikin gaggawa, bayan isa majalisar da safe, sannan aka gaggauta kai shi asibiti, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Kuma za a binne marigayi Aminu Sa’adu misalin karfe 6:00 na yamma, bisa tsarin addinin Musulunci, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here