NSCDC ta tabbatar da harin ‘yan ta’adda kan sansanin su a Neja

images 10 4 678x430

Hukumar tsaro ta Civil Depence ta Ƙasa (NSCDC) ta tabbatar da harin ‘yan ta’adda kan ma’aikatan ta da ke sansanin Wawa a Ƙaramar Hukumar Borgu, Jihar Niger.

Suberu Siyaka-Aniviye, Kwamandan hukumar a jihar, ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a Minna ranar Laraba, inda ya ce babu wanda ya rasa ransa.

Siyaka-Aniviye ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun zo da yawa a tsakiyar dare, amma basu iya gudanar da aikinsu ba saboda shirin da kuma saurin martanin ma’aikatan dake aiki.

Kwamandan ya ce ma’aikatan sun yi ƙoƙarin tursasawa ‘yan ta’addan, amma lamarin ya yi wuya saboda yawan su da kuma duhun wurin.

Karanta: Cikakken jadawali: EFCC ta alaƙanta tsohon AGF Malami da kadarori 41 a Kano, FCT da Kebbi da darajarsu ta haura Naira Biliyan 212

Ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun yi amfani da fitilu don gano wanda ke zuwa kafin su bude wuta, lamarin da ya tilastawa ma’aikatan su yi amfani da dabarun boya.

Siyaka-Aniviye ya ce ma’aikatan sun bar motar aiki yayin da suke neman tsira, amma ‘yan ta’addan sun dauka suna ciki suka ci gaba da harbi a kai.

Ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun sace wasu kayayyaki na sirri yayin harin, kuma sun shiga gidaje suka dauki kaya kamar tufafi, wayoyin salula da sauran kayan aiki, tare da tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun dauki bindiga daya yayin da mai ita ke kokarin boye jiki.

Kwamandan ya jaddada cewa babu wani ma’aikaci da ya rasa rai ko ya ji rauni mai tsanani, ko da yake wasu sun samu raunuka kadan yayin da suke neman tsira.

Ya ce Kwamandan-Janar na NSCDC, Mista Ahmed Audi, ya tura tawagar dabaru zuwa Niger domin gudanar da bincike da kuma karfafa tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here