Cikakken jadawali: EFCC ta alaƙanta tsohon AGF Malami da kadarori 41 a Kano, FCT da Kebbi da darajarsu ta haura Naira Biliyan 212

Malami

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta gano kadarori guda 41 da ake alaƙantawa da tsohon babban lauyan ƙasa kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, da ɗansa Abdulaziz Malami.

Kadarorin, waɗanda suka haɗa da otel-otel, makarantu, gine-ginen zama, filaye da gidan buga takardu, suna a jihohin Kebbi da Kano da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, inda aka kiyasta jimillar darajarsu da kusan Naira Biliyan 212.89.

Bisa wani takarda da jaridar Premium Times ta samu, bayanin ya zo ne a daidai lokacin da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta gudanar da bincike a gidaje da ofisoshinsa da ke Abuja da Jihar Kebbi, a matsayin wani ɓangare na binciken da ake ci gaba da yi kan zargin aikata laifukan kuɗi.

An ƙiyasta darajar kadarorin da ke Jihar Kebbi da N162,195,950,000, yayin da aka ce kadarorin da ke Jihar Kano sun kai darajar N16,011,800,000, sannan kuma aka sanya darajar kadarorin da ke Babban Birnin Tarayya Abuja a kan N34,685,000,000.

Kadarorin Jihar Kebbi

Jimillar ƙimantawa: N162,195,950,000.00

Jami’ar Rayhaan da harkokin Ilimi

Gidan dindindin na Jami’ar Rayhaan: N56,000,000,000.00

Gidan wucin-gadi na Jami’ar Rayhaan: N37,800,000,000.00

Wuri na uku na Jami’ar Rayhaan: N2,450,000,000.00

Gidan mataimakin shugaban jami’a na Jami’ar Rayhaan: N490,000,000.00

Makarantar Rayhaan Model Academy: N11,200,000,000.00

Makarantar firamare da sakandare ta Rayhaan: N8,750,000,000.00

Masana’antar Rayhaan Agro Allied da Kasuwanci

Gine-ginen masana’anta: N4,200,000,000.00

Na’urori da rukunin injinan masana’anta: N10,500,000,000.00

Masallacin masana’anta: N2,450,000,000.00

Gidajen ma’aikatan Rayhaan Mill (raka’a 10): N1,487,500,000.00

Ginin Rayhaan Bustan: N3,150,000,000.00

Maɗaba’a ta bugawa: N1,050,000,000.00

Gidan ajiye tankokin makamashi na Al-Afiya Energy: N2,450,000,000.00

Tsarin kamfanin Amasdul Oil and Gas Ltd: N1,050,000,000.00

Rediyon Rayhaan: N78,750,000.00

Kadarorin Alamar Azbir

Otal ɗin Azbir: N10,325,000,000.00

Dakin baje kolin kaya: N581,000,000.00

Lambuna: N392,000,000.00

Masallaci: N252,000,000.00

Kayan sawa na Azbir: N350,000,000.00

Magunguna da babban shago na Azbir: N175,000,000.00

Gidaje da Ginshikai

Gidan Malami a GRA: N350,000,000.00

Gidan Malami bayan Mobil: N490,000,000.00

Gidan Malami bayan makabarta: N350,000,000.00

Gidan Abdulaziz (ɗa na fari): N1,659,000,000.00

Gidan Ahbiru (ɗa na biyu): N2,989,000,000.00

Ginin ƙungiyar goyon bayan Malami ADC: N210,000,000.00

Ginin gidauniyar Kadi Malami: N56,000,000.00

Gidan tsaron Rayhaan: N245,700,000.00

Gini bene uku da ba a kammala ba: N665,000,000.00

Kadarorin Jihar Kano

Jimillar ƙimantawa: N16,011,800,000.00

Otal ɗin Zeennoor: N11,200,000,000.00

Masallacin Zeennoor: N84,000,000.00

Tsohon ginin otal na Zeennoor: N280,000,000.00

Otal ɗin Rayhaan Kano: N2,240,000,000.00

Dakin motsa jiki na Rayhaan Kano: N1,225,000,000.00

Gidan mata (Hanyar Ahmadu Bello, Kano): N982,800,000.00

Kadarorin Babban Birnin Tarayya Abuja

Jimillar ƙimanta: N34,685,000,000.00

Gida mai bene biyu a Titin Amazon, Maitama: N5,950,000,000.00

Otal ɗin Meethaq (reshen Jabi): N8,400,000,000.00

Otal ɗin Meethaq (reshen Maitama): N12,950,000,000.00

Raka’o’in bungalow 42 a unguwar Efab: N385,000,000.00

Otal-otal na Harmonia, Area 11 Garki: N7,000,000,000.00

Jimillar dukkannin ƙimar: N212,892,750,000

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here