Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da wasu sabbin naɗe-naɗe da kuma ƙarin girma a muƙamai, domin ƙarfafa harkokin shugabanci da inganta ayyukan hidima a muhimman sassa na gwamnati.
Wannan ya fito ne daga cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba a Kano, inda ya bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na bunƙasa aiki da nagartar shugabanci.
Sanarwar ta nuna cewa daga cikin waɗanda aka naɗa akwai Abdulkadir Kankarofi a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin jin-ƙai, yayin da aka naɗa Hajiya Aisha Tamburawa a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan yaɗa sahihan bayanai masu amfani.
Haka kuma, gwamnan ya amince da naɗa Alhaji Mukhtar Yusuf a matsayin babban darakta na hukumar ilkirkire- kirkire da gine-ginen albarkatun ruwa ta jihar Kano, sannan aka naɗa Dakta Mukhtar Maisudan a matsayin sakataren zartarwa na hukumar bada tallafin karatu ta jihar Kano.
Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Alhaji Abba Kankarofi a matsayin babban darakta na hukumar kula da gyaran hanyoyi ta jihar Kano, da kuma Musayyib Ungoggo a matsayin babban darakta na gidan namun daji na jihar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci dukkan waɗanda aka naɗa da su nuna jajircewa, gaskiya da riƙon amana a ayyukansu, tare da sadaukar da kai wajen yi wa al’ummar jihar Kano hidima, daidai da manufofin ajandar Kano ta farko.













































