Majalisar Wakilai ta nemi a gabatar da shaidar biyan kwangila na Naira tiriliyan 2.4

Accountant General of the Federation Shamseldeen Babatunde Ogunjimi 750x430

Majalisar Wakilai ta nemi Ofishin Akanta-Janar na Ƙasa da ya gabatar da hujjojin biyan kudaden kwangila na Naira tiriliyan 2.4 da gwamnatin tarayya ta amince da su.

Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu, ne ya bayyana haka yayin hira da ’yan jarida bayan ganawa da ’yan kwangila a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa taron ya kasance wani ɓangare na jerin tattaunawa da Majalisar ke yi domin shawo kan zanga-zangar da ’yan kwangila ke yi saboda rashin biyan su kuɗin ayyukan da suka kammala.

Dan majalisar ya ce bukatar ta zama dole ne domin wasu daga cikin ’yan kwangila na ƙorafin ba a biya su bashin da ake binsu ba.

Ya ce jami’an gwamnati sun tabbatar da cewa Naira tiriliyan 2.4 aka amince a biya, kuma daga cikinsa an riga an biya, sai Naira biliyan 160 kawai suka rage.

Ya kara da cewa akwai ƙarin Naira biliyan 760 da aka amince domin biyan sauran basussuka, wanda zai kai jimillar kudaden zuwa Naira tiriliyan 3.1.

Sai dai ya ce, ya umarci Ofishin Akanta-Janar na Ƙasa da ya gabatar da cikakken jerin sunayen wadanda aka biya domin tabbatar da gaskiya.

Kalu ya bayyana damuwarsa da cewa bai kamata gwamnati ta biya Naira tiriliyan 2.4 amma har yanzu ’yan kwangila suna ci gaba da yin zanga-zanga ba tare da ganin kudin ba.

Ya ce majalisar za ta bincika domin gano ko waɗanda aka biya su ne suke ƙorafi, ko kuwa akwai wani rashin gaskiya a cikin tsarin.

Ya kuma gargadi ’yan kwangila da su tabbatar cewa duk aikin da suka karɓi kuɗi a kai an yi shi yadda ya kamata.

Ya ce “abin ƙiyayya ne a ce an karɓi kuɗin gina asibiti amma babu asibiti, ko kuma a ce an gina makarantu amma dalibai suna karatu ƙarƙashin bishiya, ko kuma a ce an yi titunan gona amma amfanin gona na lalacewa saboda babu hanyar jigilar su zuwa birane.”

Mataimakin kakakin ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa Majalisar za ta ci gaba da matsa wa gwamnati lamba ta cika alkawuran ta, tare da riƙe ’yan kwangila da alhakin ingancin ayyukansu. (kamfanin dillancin labarai na ƙasa.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here