Kungiyar kwadago ta ƙasa NLC da kuma ƙungiyar ƙwadago ta TUC sun tabbatar da ci gaba da ba sa goyon bayansu ga ma’aikatan Babban Birnin Tarayya FCT da ke tsaka da yajin aiki.
Ƙungiyoyin sun sanar da wannan matsaya ne ta cikin wata sanarwa da mukaddashin babban sakataren NLC, Benson Upah, da babban sakataren TUC, Nuhu Toro, suka sanya wa hannu tare, wadda aka fitar a ranar Laraba a Abuja.
Ƙungiyoyin sun tunatar da cewa duk da umarnin da kotun masana’antu ta ƙasa NIC ta bayar na dakatar da yajin aikin, kotun ba ta bayar da wani umarnin hana ma’aikatan ci gaba da fafutukar neman haƙƙinsu ba.
Sun jaddada cewa yajin aikin zai ci gaba har sai ministan Abuja, Nyesom Wike, ya shiga tattaunawa mai ma’ana da ma’aikatan da ƙungiyoyin ƙwadago.
Ƙungiyoyin sun nuna cewa ba za su zuba ido ana gallaza wa ma’aikata, ana tozarta su da cin zarafinsu ba saboda neman haƙƙoƙinsu na halal, tare da tsayawa tsayin daka kan kare martabar ma’aikatan.
NLC da TUC sun sake tabbatar da cikakken goyon bayansu ga ma’aikatan Abuja, inda suka buƙace su da su ci gaba da kare haƙƙoƙinsu cikin jajircewa, mutunci da haɗin kai.
Ƙungiyoyin sun kuma yi Allah wadai da abin da suka bayyana a matsayin tsoratarwa, cin zarafi da rashin adalci da ake nuna wa ma’aikatan Abuja, suna danganta hakan da matakan ministan, tare da sukar hukuncin kotun masana’antu ta ƙasa NIC da suka ce ya karkata gefe guda, duk da cewa sun jaddada biyayyarsu ga doka da kare haƙƙin ma’aikata.













































