Gwamnatin jihar Kano ta sassauta dokar hana fita da ta sanya a jihar daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.
Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Dogo Salman ne ya sanar da hakan a ranar Talata jim kadan bayan wani taron tsaro na hadin gwiwa da Gwamna Abba Yusuf a gidan gwamnati.
Salman ya jaddada kudirin gwamnati na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar tare da sassauta dokar hana zirga-zirgar jama’a don baiwa mazauna yankin damar ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.
Ya kara da cewa matakin sassauta sa’o’in hana fita ya nuna yadda tsaro ya inganta da kuma kokarin jami’an tsaro na maido da zaman lafiya a Kano.
Gwamna Yusuf ya kuma bukaci ‘yan jihar da su baiwa jami’an tsaro hadin kai tare da bin ka’idojin dokar hana fita domin tabbatar da ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.