Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Isa-Sabon Birni a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Abdulkadir Jelani Danbuga, ya rasu.
Wani mamba mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta Kudu a majalisar dokokin jihar Sokoto, Aminu Almustapha (aka Boza) ya tabbatar da rasuwar.
A cewar Boza, dan majalisar tarayya ya rasu ne da misalin karfe 12:30 na safiyar ranar Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya.
“Za a kai gawar sa zuwa Masallacin kasa domin yin wanka, daga nan kuma za a kai gawar Sokoto domin binne shi da misalin karfe 11 na safe,”
in ji Almustapha. Danbuga ya rasu ya bar mata biyu, ‘ya’ya da jikoki da dama.
Aminiya