‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Hudu A Jihar Nasarawa

Gunmen
Gunmen

A ranar Litinin da daddare ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu dalibai hudu na jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK).

Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:30 na dare, kusa da Angwan Kare bayan BCG.

Daliban da aka sace an bayyana sunayensu da Rahila Hanya – SLT 100Level, Josephine Gershon – Computer Science 100Level, Rosemary Samuel – Business Administration 100Level, da Goodness Samuel – Geography 100Level.

Da yake mayar da martani kan lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, a ranar Talata, shugaban kungiyar daliban, Kwamared Oshafu Nuhu Abdulrahman, ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika, inda ya bukaci daliban da su kwantar da hankalinsu tare da yin addu’a domin ana kokarin ganin an sako su cikin koshin lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here