Dan gwagwarmayar Yarbawa, Sunday Igboho ya sake samun cikakken ‘yancinsa a jamhuriyar Benin da ke makwabciyar Najeriya.
Farfesa Banji Akintoye, shugaban kungiyar Yarabawa, ya ce an sako Igboho ne a ranar Lahadin da ta gabata, kuma ya tafi kasar Jamus domin shiga cikin iyalansa.
An kama Igboho ne a watan Yulin 2021, a lokacin da yake shirin shiga jirgi zuwa Jamus, makonni bayan da ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hari da jami’an tsaro suka kai masa a gidansa na Ibadan.
Daga baya hukumar DSS ta bayyana cewa ana neman sa.











































