Yadda jirgin sama ya samu tangarda a Abuja – NCAA, FAAN 

Cargo Plane 750x430 (1)

Ayyuka a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja, sun samu cikas a ranar Laraba bayan wani jirgin kaya ya sauka daga hanya.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) sun tabbatar da cewa duk ma’aikatan jirgin kaya na Allied Air Cargo, mai rijista 5N-JRT, sun tsira lafiya ba tare da wani rauni ba.

Michael Achimugu, Daraktan Kare Hakkin Masu Amfani da Sufurin Jiragen Sama na NCAA, ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da jan hankalin fasinjoji su kasance masu hakuri, yana mai cewa, “Saboda wani al’amari da ya faru a filin jirgin sama na Abuja, za a iya samun jinkiri a wasu tashoshi, don Allah ku kasance masu hakuri da natsuwa.”

Kakakin FAAN, Obiageli Orah, ya bayyana cewa jirgin ya kauce daga Hanya ta 22 da misalin karfe 10:05 na safe. Kungiyar bada agajin gaggawa da masu binciken hadurra sun garzaya wurin domin daukar matakin gaggawa.

Ana ci gaba da kokarin gyara hanyar jirgin, tare da tabbacin FAAN cewa ayyuka za su dawo kamar yadda aka saba nan ba da jimawa ba.

FAAN ta kuma roki jama’a su guji yada jita-jita, tana mai cewa Hukumar Bincike kan Hadurran Jiragen Sama ta Najeriya (NSIB) na gudanar da bincike na farko.

Hukumomin jiragen sama sun gode wa jama’a da masu ruwa da tsaki bisa goyon bayansu da hakurinsu a wannan lokaci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here