Kotun Jihar Kano ta tsayar da ranar 13 ga Fabrairu, 2025, domin sauraron dukkan koke-koke game da shari’ar zargin cin hanci da almundahana da ake yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, da wasu mutum bakwai.
Gwamnatin Jihar Kano ce ta shigar da karar mai dauke da tuhume-tuhume guda takwas kan Ganduje da matarsa, Hafsat Umar, bisa zargin karbar cin hanci da almubazzaranci da kudaden al’umma da suka kai biliyoyin naira.
Sauran wadanda ake tuhuma sun hada da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited, da Lasage General Enterprises Limited.
A zaman kotun da aka yi ranar Laraba, lauyan da ke kare Ganduje, matarsa, da Umar, M.N. Duru, SAN, ya nemi a janye wata bukata da suka gabatar