Jami’ar tarayya ta Kashere ta musanta zargin harin ‘yan bindiga

FUK

Jami’ar tarayya ta Kashere da ke Jihar Gombe ta musanta rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke zargin cewa ‘yan bindiga sun kai hari a harabar jami’ar.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da jami’ar ta fitar ga manema labarai, inda ta fayyace cewa rahoton ba shi da tushe kuma an ƙirƙire shi ne domin tayar da hankalin ɗalibai da al’umma tare da kawo cikas ga jarabawar zangon karatu na farko da ke gudana.

Jami’ar ta tabbatar da cewa babu wani lamari makamancin haka da ya faru a cikin al’ummar jami’ar, tana mai kira ga jama’a da su yi watsi gaba ɗaya da bayanan ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta na internet.

A cewar jami’ar, abin da aka danganta da jami’ar a cikin rahoton da ya bazu ba shi da alaƙa da makarantar, illa rikici ne na cikin gida tsakanin matasan ƙauyukan Jauro Buba da Garin Rigiya da ke yankin.

Jami’ar ta kuma bayyana cewa hukumomin tsaro sun shawo kan lamarin gaba ɗaya, inda rundunar ‘yan sanda ta daidaita yanayin tsaro, lamarin da ya sa zaman lafiya ya dawo yadda ya dace.

Haka kuma, jami’ar ta tabbatar da cewa tana aiki tare da hukumomin tsaro ciki har da ‘yan sanda, kuma harkokin karatu na ci gaba kamar yadda aka saba ba tare da wata tangarda ba, tare da tabbatar wa iyaye, masu kula da ɗalibai da al’umma cewa babu wani abin firgici.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here