Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki a kasar Türkiye

Tinubu arrival 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dawo Abuja da dare bayan kammala ziyarar aiki ta ƙasa da ya kai zuwa Türkiye.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa jirgin shugaban ƙasa ya sauka a sashen shugaban ƙasa na filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe takwas da mintuna hamsin da shida na dare.

Ziyarar aikin ta ƙasa, wadda ta fara a farkon mako, ta ƙunshi tattaunawa ta ɓangarori biyu tsakanin shugaban Najeriya da shugaban ƙasar Türkiye, Recep Tayyip Erdoğan.

Ziyarar ta kai ga sanya hannu kan yarjejeniyoyi tara da suka shafi tsaro, makamashi, kariya, bincike da sauran muhimman fannoni na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

Haka kuma, shugabannin biyu sun duba muhimman abubuwan da suka shafi haɗin kai da ke da nufin ƙarfafa alaƙar Najeriya da Türkiye a fannoni daban-daban na muradun juna.

Tawagar shugaban ƙasar da suka raka shi sun haɗa da ministoci da manyan jami’an gwamnatoci, waɗanda suka shiga tattaunawar ɓangarori biyu da aka gudanar a yayin ziyarar.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here