Ƙungiyar haɗin gwiwar matan musulmi a Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta sake duba kayan aikin hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima NYSC domin tabbatar da cikakken tsarin shigar da mata mambobin hidimar ƙasa musulmi a cikin tsarin.
An gabatar da wannan buƙata a yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja domin bikin ranar Hijabi ta Duniya ta shekarar 2026, inda wata mamba a ƙungiyar, Firdausi Amasa, ta yi jawabi kan batun.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa ranar hijabi ta duniya ana gudanar da ita duk shekara a matsayin wani dandalin duniya da ke bayyana muhimmanci da darajar suturar mace musulma tare da ƙarfafa fahimta a tsakanin al’umma daban-daban.
An kafa wannan shiri ne a 2013 ta hannun Nazma Khan, bayan ta fuskanci kalubale na baki da na jiki sakamakon zaɓinta na sanya hijabi, lamarin da ya zamo tushen ƙarfafa gwiwa ga mata a sassa da dama na Duniya.
Amasa ta nuna cewa kayan aikin hukumar NYSC na yanzu ba su dace da mata mambobin hidimar ƙasa musulmi ba, inda ta jaddada buƙatar sake fasalin dokar tufafi domin bai wa mata musulmi da sauran masu bukata damar yin hidima cikin mutunci da jin daɗi.
Ta kuma nuna buƙatar majalisar dokoki ta ƙasa ta gaggauta amincewa da dokokin da ke kare mutane daga wariya bisa kamanni ko addini, tare da buƙatar al’umma su tallafa wa mata da suka koma addinin musulunci da ke fuskantar ƙalubale daga iyalai da muhallansu, domin gina kwarin gwiwa da haɗin kai.
Bugu da ƙari, ta yi kira da a samar da shirye-shiryen al’umma da za su ƙarfafa mata masu sanya hijabi ta hanyar jagoranci, koyar da sana’o’i da horarwa, tare da buƙatar hukumomin gwamnati, makarantu da kamfanoni masu zaman kansu su aiwatar da tsare-tsaren da ke girmama ’yancin addini da rawar da mata ke takawa wajen ci gaban ƙasa.
A nata ɓangaren, Zainab Umar ta yaba wa ma’aikatar ilimi ta tarayya, hukumar NYSC, majalisar koyar da shari’a, kotun koli ta Najeriya, rundunar sojojin ƙasa, rundunar ’yan sanda da sauran hukumomi bisa goyon bayan da suke bai wa mata musulmi, lamarin da ke ƙarfafa mutunci, haɗin kai da ci gaba.
NAN













































