Majalisar dokoki ta fara bincike kan rushe wasu shaguna 500 a Kano

Kano State House of Assembly 700x430

Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa wani kwamiti mai mutum bakwai da zai binciki rushe wasu shaguna sama da 500 a kasuwar Rano da ke karamar hukumar Rano.

Matakin ya biyo bayan wani kudiri na gaggawa da dan majalisa mai wakiltar mazabar Rano, Ibrahim Muhammad ya gabatar wanda ya nuna damuwarsa kan yadda rushe shagunan ta shafi ‘yan kasuwar yankin da kuma al’umma.

Yana mai bayyana rushe su a matsayin abin takaici, inda ya bukaci majalisar da ta shiga tsakani tare da binciken halin da ake ciki.

Muhammad ya yi kira da a yi karin haske kan dalilan da suka haddasa rushe ginin, inda ya yi nuni da irin matsanancin halin kuncin da ‘yan kasuwar da abin ya shafa za su fuskanta, wadanda suka yi hasarar dukiyar su, sakamakon rashin ba su cikakkiyar sanarwa.

Karanta: Kisan Rimin Zakara: Gwamna Yusuf ya umarci BUK da ta dakatar da aikin Rusau

Da yake mayar da martani kan kudirin, shugaban majalisar, Alhaji Ismail Falgore ya bayar da umarnin a kafa kwamitin mutane bakwai domin gudanar da bincike kan lamarin.

A cewarsa, kwamitin zai kasance karkashin mataimakin shugaban majalisar, Muhammad Bello Butu-Butu kuma ana sa ran zai mika sakamakon bincikensa cikin mako guda.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa rusau da aka yi a makon da ya gabata ya janyo cece-kuce daga ‘yan kasuwarda mazauna garin na Rano.

Jama’a da dama sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta biya diyya tare da mayar da ‘yan kasuwar da abin ya shafa matsugunninsu. (NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here