Yau ake sa ran fara isowar yan Najeriyan da suka makale a Sudan zuwa Abuja

1683121857991
1683121857991

Aƙalla ƴan Najeriya da suka maƙale a Sudan, mutum 354 waɗanda aka kwaso su daga ƙasar ake sa ran isowar su, gida Najeriya a yau ranar Laraba. Jaridar Tribune tace a bisa tsarin da aka yi, jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya, NAF C-130 zai ɗauko mutum 80, yayin da jirgin kamfanin jirgin sama na Air Peace zai ɗauko mutum 274.

Ƴan Najeriyan dai za a kwaso su ne a Aswan cikin ƙasar Egypt akan jiragen rundunar sojin saman Najeriya, (NAF C-130)da kuma jirgin kamfanin Air Peace.

Jirgin rundunar sojin saman na NAF C-130, yana a ƙasar Egypt tun ranar Lahadi, a yayin da aka tsayar da jirgin Air Peace a Najeriya har zuwa lokacin da hukumomin ƙasar Egypt za su sahale ƴan Najeriyan su shigo cikin ƙasar.

Shugabar hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NiDCom), Hon. Abike Dabiri-Erewa, ta tabbatar da halin da ake ciki a shafinta na Twitter. Hon. Dabiri-Erewa, wacce tare da ministan harkokin ƙasashen waje suka tattauna da kakakin majalisar wakilai, Hon. Femi Gbajabiamila, bayan kammala zaman majalisar na ranar Talata, ta tabbatar da dukkanin ƴan Najeriyan sun isa tashar jirgin ruwan Sudan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here