An kai hari ofishin jakandancin Saudiyya a Sudan

1683121857991
1683121857991

Wata ƙungiya da ke ɗauke da makamai ta yi wa ofishin jakadancin Saudiyya da ke Khartoum ƙawanya.

A cikin wata sanarwa da ma`aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar, ta ce ƙungiyar masu ɗauke da makamai sun lalata kayan aiki da kyamarori.

Sanarwar ta kuma ce maharan sun ƙwace wasu daga cikin kadarorin ma`aikatar, tare da lalata na`urori da intanet din ofishin.

Saudiyya ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan wannan aika-aikar tare da yin kira da a tabbatar da mutunta tsarin diplomasiyya ta hanyar hukunta waɗanda suka aikita laifin

Masarautar ta sake jaddata kiran dakatar da fada tsakanin sojojin ƙasar, tare da kawo ƙarshen tashe tashen hankula, da kuma ba da kariya ga jami’an diflomasiyya da fararen hula.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here