Wasu ‘yan bindiga a jihar Kaduna sun farmaki wasu makarantun Firamare da Sakandiren garin Kuriga na karamar hukumar Chikun da safiyar yau Alhamis tare da sace daliban da adadinsu ya zarta 200.
Wani mazaunin garin Aminu Kuriga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kutsa kai cikin makarantar ne da misalin karfe 8 na safiya lokacin da ake tsaka da daukar darasi tare da kwashe daliban.
Karin labari: An yi amfani da sa hannun Buhari na bogi don cire dala miliyan 6.2 a CBN – Bincike
A cewar Aminu Kuriga baya ga daliban ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da shugaban sashen karamar Sakandiren da wasu malamai.
Bayanai dai na cewa har zuwa yanzu babu cikakken alkaluman yawan dalibai da malamai da aka yi awon gaba da su a wannan farmaki.
Karin labari: Yadda ‘yan bindiga suka kashe makiyaya da shanu 35 a jihar Filato
Ko a watanni biyu da suka wuce ‘yan bindigar sun kai makamancin farmaki makarantar tare da kashe shugaban sashen babban Sakandire.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yan bindiga ke farmakar makarantu a jihar ta Kaduna ba, wanda a wasu lokutan ke kaiwa ga asarar dimbin rayuka.
Har zuwa yanzu dai babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar da ke tabbatar da faruwar lamarin ko kuma yunkurin kubutar da Daliban.