An yi amfani da sa hannun Buhari na bogi don cire dala miliyan 6.2 a CBN – Bincike

Buhari, Emefiele,bincike, kudi, EFCC, dala, miliyan
An ci gaba da shari'ar da ake yi wa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda aka tabbatarwa kotu cewa binciken kimiyya ya...

An ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda aka tabbatarwa kotu cewa binciken kimiyya ya nuna cewa an yi amfani da sa hannun bogi na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wajen cire kuɗi dala miliyan 6.2 don daukar nauyin masu sanya idanu na ƙetare a zaɓukan ƙasar.

Wani shaida da EFCC ta kira, mai suna Bamaiyi Meriga ya tabbatarwa kotu ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Hamza Muazu cewa binciken kimiyya da aka yi wa takardun da aka sanya hannu a kansu don cire kudin ya nuna cewa sa hannu da hatimi da aka yi amfani da su wajen cire kudin ba daidai suke da na ainihi ba.

Karin labari: “Herbert Wigwe ya taimake ni bayan sauke ni daga sarkin Kano” – Sanusi II

Ya kuma tabbatar da cewa sa hannun ba na tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ne, kuma ba na tsohon sakataren gamnatin tarayya, Boss Mustapha ba ne.

An gabatarwa alƙalin da ke jagorantar shari’ar takardun biyu, masu ɗauke da umarnin shugaban ƙasa a matsayin shaida, sannan kuma ya amince da su.

Bayan da lauyoyin Emefiele suka nuna ƙorafinsu game da takardun, shaidar ya ce shi ba ma’aikacin EFCC ba ne kuma ba hukumar ce ke biyan sa ba.

Karin labari: Donald Trump zai sake gurfana a gaban kotu ranar Larabar nan

Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa, ya nuna rashin amincewarsa da shaidar, yana mai cewa shaidar ya yaudari kotun ne don kaucewa tambayoyin da za’a yi masa.

To sai dai lauyan masu shigar da ƙara, Rotimi Oyedepo, bai ji dadin kalaman lauyan wanda ake ƙarar ba.

Emefiele na fuskantar shari’a a kotun kan laifuka 20 da suka ƙunshi zargin cin hanci da haɗin baki da cin amana da amfani da sa hannun bogi wajen cire kudi har dala 6,230,000.

Ana zargin sa da sa hannun bogi na tsohon sakataren gwamnatin ƙasar Boss Mustapha wajen ciye kuɗin ta hanyar da ba ta dace ba kamar yadda BBC ta rawaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here