Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump zai gurfana a wata kotu da ke birnin Washington domin sanin matsayinsa kan ko yana da kariya daga fuskantar shari’a kan manyan laifuka ko a’a.
Ana sa ran lauyoyinsa za su shaida wa kotu cewa matsayinsa na wanda ya taba shugabancin kasar ya ba shi kariya daga fuskantar shari’a.
Karanta wannan: Majalisar Wakilan Amurka za ta fara shirin tsige shugaba Joe Biden
Hukuncin da kotu za ta yanke kan wannan shari’a zai shafi sauran shari’o’i da ake yi wa Mista Trump.
Ana sa ran sai nan gaba ne kotu za ta sanar da hukuncin da ta yanke kan karar.