Gwamnatin Najeriya ta ce ma’aikatan gwamnati waɗanda suke da lambar ɗan ƙasa ta NIN ne za a bai wa damar sayen shinkafar da gwamnatin za ta sayar a farashi mai rahusa.
Ministan Noma, Abubakar Kyari ne ya sanar da hakan, inda ya ce hakan zai taimaka wajen rage ci da zuci da kuma saye abincin a kasuwa da ma rage tsadar abincin a kasuwannin Najeriya.
Abubakar Kyari ya ce a ƙarƙashin tsarin, “buhu ɗaya kawai mutum zai samu.”
Ya ce buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 za a sayar a farashin Naira 40,000 a cikin shirin gwamnatin na rage raɗaɗin tsadar kayan masarufi.
Gidan talbijin na Channels ya ambato ministan na cewa sai wanda ya mallaki shaidar ɗan ƙasa wato NIN ne kawai zai samu damar sayen shinkafar.
Ya ce an saki tan 42,000 na kayan masarufi, da kuma tan 30,000 na shinkafa wanda za a sayar wa ƴan Najeriya.
Ya ce ana sa ran fitar da abincin na gwamnati zai sa farashin abincin ya sauka a kasuwanni.
Darakta, ɓangaren abinci da tsare-tsaren tanadi na ma’aikatar, Haruna Sule Abutu ya bayyana sharaɗin da za a cika domin samun damar sayan abincin kamar haka:
Ya ce idan mutum ya zo wurin sayar da shinkafar da abubuwa guda uku, za a tantance shi, sai a ba shi wata lamba da rasitin da mutum zai kai wajen da ake karɓa ya ɗauko shinkafarsa.
Ya ƙara da cewa a jikin rasit ɗin kowa akwai lokaci da wajen da zai je ya ɗauki tasa shinkafar.