Biyo bayan wani faifan bidiyo da aka ce na Sarkin ‘yan fashin, Bello Turji, na neman sasantawa da Gwamnatin Tarayya, wata kungiya mai suna Dattawan Arewa, ta gargadi Shugaba Bola Tinubu da ya yi watsi da zaratan sa.
Shugaban kungiyar dattawan Arewa ta Arewa maso Yamma, Alhaji Mustafa Dutsinma, a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna ranar Alhamis, ya yi gargadi kan duk wani yunkuri na sasantawa da masu alaka da ‘yan fashi.
A cewarsa, a halin yanzu hankulan jama’a ya tashi, kuma sun samu kwarin gwiwa da farin ciki da ayyukan soji.
Ya ce Bello Turji yana yin kamar ya shirya sulhu ne kawai, duba da irin yawan rayukan da shi da ‘yan kungiyarsa suka kashe a ‘yan shekarun da suka gabata na ‘yan fashi da makami a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
“Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa Shugaba Tinubu na tunanin sasantawa da ’yan fashin nan, Turji, da kuma tawagarsa.
Dutsinma ya ce “Muna ba da shawara mai karfi kan wannan matakin, domin zai kafa tarihi mai hatsari tare da kawo cikas ga kokarin gwamnati na yaki da ‘yan fashi.”
“Muna ba da shawara mai karfi game da wannan matakin, domin zai kafa tarihi mai hatsari tare da kawo cikas ga kokarin gwamnati na yaki da ‘yan fashi,” in ji Dutsinma.
Ya kuma jaddada cewa yin sulhu da wadanda suka aikata munanan laifuka a kan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, zai zama cin amanar jama’a.
A yayin da yake yaba wa ayyukan soji da ke gudana zuwa yanzu a wasu kauyukan Shinkafi da Jibia, musamman hare-hare ta sama da ta kasa, Dutsinma ya bukaci sojojin da su ci gaba da kai farmakin domin samun sakamako mai inganci.
Ya ce yin sulhu da ‘yan fashin zai kasance tamkar dirar mikiya ne ga wadanda abin ya shafa da iyalansu, wadanda suka sha wahala da asara mara misaltuwa tare da neman a tabbatar da adalci, a kuma hukunta wadanda suka aikata wannan ta’asa.
Shugaban ya ce mayar da karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, da hafsan hafsoshin tsaro da sauran hafsoshin tsaro da manyan sojoji suka yi zuwa yankunan da ke fama da rikici a arewacin kasar ya nuna irin yadda gwamnatin tarayya ta himmatu wajen ganin an magance matsalar ‘yan bindiga.