Hukumar kiyaye haddura ta tarayya (FRSC) ta kaddamar da wata manhaja ta wayar hannu da Tsarin Bayar da Rahoto ta Kasa (NACRIS) don magance hadurran ababen hawa da sauran batutuwan da suka shafi kiyaye lafiyar titi a fadin kasar.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sen. George Akume, da yake jawabi a wajen kaddamar da taron ranar Alhamis a Abuja, ya bayyana nasarar da aka samu a matsayin wani ci gaba a tarihin hukumar FRSC.
Ya bayyana cewa manhajar zata taimaka sosi wajan rage hadura.
A cewarsa, manhajar wayar hannu da NACRIS za su wayar da kan direbobi da fasinjoji kan abubuwan da za su iya haddasa hadurran ababen hawa.