Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a ranar Alhamis ta tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da jikkatar mutum uku a wani bene mai hawa biyu da ya rufta a unguwar Noman’s Land
dake karamar hukumar Fagge da ke Kano.
Dokta Nuraddeen Abdullahi, kodinetan hukumar NEMA reshen jihar Kano, ya tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Kano.
Ya ce, “Hukumar ta samu kiran waya a yau da misalin karfe 2:00 na safe cewa wani bene mai hawa biyu ya ruguje a unguwar Noman’s Land Quarters, Kano.
“Da samun bayanan, mun aika da tawagarmu da gaggawa wurin da abin ya faru.
“Mutane biyar da tawagarmu ta ceto sun hada da miji da mata da ‘ya’ya uku; Daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, an tabbatar da mutuwar yaran uku, yayin da aka garzaya da ma’auratan zuwa asibitin kwararru na rundunar soji da ke Kano domin yi musu magani,” inji Abdullahi.
Ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da aikin ceto mutanen da suka makale a ginin.
NAN ta ruwaito cewa hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ’yan sanda, Red Cross, NSCDC, SEMA da sauran su na daga cikin tawagar da ta gudanar da aikin ceton.(NAN)