Gwamnonin Arewacin Najeriya 19 sun yabawa Gwamntin Tarayya bisa sahalewa a girke sabbin Jiragen yaki da Yan ta’adda samfurin super tucano awasu bangarorin arewa dake famada matsalar tsaro.
Shugaban kungiyar gwamnonin arewa Kuma Gwamnan FILATO Simon Lalong ya bayyana haka ataron manema labarai bayan wata ganawar sirri da shugaban kasa.
Gwamna Lalong ya bayyana jin dadi da farin ciki amadadin daukacin gwamnonin Arewacin Najeriya bisa bayyana Yan bindiga da Sunan Yan ta’adda da Gwamntin tayi
“Batun tsaro hakikanin gaskiya mun fara ganin sabbin cigaba adukkan alamuran damuke dauka tun a shekarar bara, Kuma kunsani mun kagu matuka muga yadda wadannan jiragen yaki samfurin super tucano ke gudanar da aikace aikacen su” Inji Lalong
“Kuma sojoji sun shirya tsaf domin fara aiwatar wannan tsare tsaren yaki da Yan ta’adda a jihohin arewa” Inji Lalong
Gwamna Lalong ya bayyana bukatar daukar matakan dasuka dace domin dakile matsalar Yan ta’adda da sauran masu aikata lefuka akokarin dakile Yan ta’adda domin baiwa manoma damar samar da isasshen abinci a jihohin
Gwamnan daganan ya jaddada bukatar dukkanin gwamnonin arewa dasu cigaba da hada Kai da sarakuna da sauran masu rikeda mukaman gargajiya da Yan sintiri da kare yankunan su da al’ummun su daga kowacce irin barazanar tsaro.













































