Kotu ta tura Emefiele zuwa gidan yari

Court Grants Former CBN Governor Emefiele Bail 750x430.jpeg 1
Court Grants Former CBN Governor Emefiele Bail 750x430.jpeg 1

Wata babbar kotu da ke zaman ta a Abuja, ta bayar da umarnin tasa ƙeyar tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, zuwa gidan yarin Kuje kafin yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa.

Emefiele dai na fuskantar zargi kan batutuwa da suka shafi harkokin kuɗi a ƙasar.

An yi ta samun cikas a zaman shari’ar kafin yanke wannan hukunci a yau Juma’a.

Alkalin kotun, Mai shari’a Hamza Muazu, ya ce yana buƙatar lokaci kaɗan don yin nazari a kan tanade-tanaden doka da kuma duba abubuwan da Emefiele ya gabatar na neman beli.

Sai dai ya bayar da umarnin a tsare Emefiele a gidan yarin Kuje da ke Abuja har sai an yanke shawara kan buƙatar neman belinsa.

Daga nan Muazu ya ɗage sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Nuwamba domin yanke hukunci kan neman belin da kuma ranar 28 ga watan Nuwamba domin fara shari’ar.

Umarnin tsare shi na zuwa ne bayan mai shari’a Olukayode Adeniyi, ya bayar da umarnin a sake shi a ranar 8 ga watan Nuwamba bayan shafe kwanaki 151 a tsare.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here