SSANU, NASU sun janye yajin aiki

SSANU NASU

Kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin ma’aikatan da ba na koyarwa a manyan makarantu, ya ce ya dakatar da yajin aikin da suke yi na tsawon wata daya, daga ranar 5 ga watan Nuwamba.

JAC ta ƙunshi Ƙungiyar NASU da Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU).

Mista Peters Adeyemi, babban sakataren kungiyar ta NASU ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Mista Mohammed Ibrahim, shugaban kungiyar SSANU ya sanya wa hannu ranar Lahadi a Abuja.

Idan za a iya tunawa JAC ta umurci mambobinta da su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar 28 ga Oktoba, domin neman rashin biyan albashin watanni hudu da kuma rashin aiwatar da wasu bukatu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here