Burkina Faso ta buƙaci sojojin Faransa su fice daga ƙasar

FB IMG 16743973258930957
FB IMG 16743973258930957

Gwamnatin soji a Burkina Faso ta buƙaci sojojin Faransa da aka girke a ƙasar da su tattara nasu inasu su bar ƙasar.

Kafar yaɗa labaran ƙasar ta ce gwamnati ta sanar da soke yarjejeniyar da ta ƙulla da su, wadda ta ba su damar zama a ƙasar, kuma tana so su fice daga ƙasar nan da wata guda.

Ko a ranar Juma’a sai da aka gudanar da boren ƙin jinin Faransa, inda wasu ke kiran kamfanin tsaro na sojin hayar Rasha na Wagner da ya taimaka wajen ceto ƙasar.

Ana zargin rundunar ta musamman mai sojojin da yawansu yakai 400 da gaza taɓuka komai wurin daƙile ayyukan masu tayar da ƙayar baya a ƙasar, wanda kuma shi ne maƙasudin girke su.

Sai dai gwamnati a Paris ta ce ba za ta daina taimaka wa Burkina Faso ba wurin wannan yaƙi, duk da ƙin jinin Faransa da ƙasar ke nunawa.

Mayaƙa masu tsatstsauran ra’ayi sun bazu a yankin shekaru goma da suka wuce, kuma bincike ya nuna cewa daga Mali suka shiga ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here