Majalisar ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ta yi Allah wadai da sabon yawaitar kashe-kashe da rashin tsaro a sassan kasar, inda ta bayyana halin da ake ciki a matsayin gangarowa cikin wani mummunan yanayi, biyo bayan kisan mutane sama da 200 a kauyen Woro da ke karamar hukumar Kaiama a Jihar Kwara.
Majalisar, wadda ke daga cikin manyan kungiyoyin Musulunci da kan yi tsokaci kan al’amuran ɗabi’a da tsaron kasa, inda ta bayyana matsayarta cikin wata sanarwa da babban sakatarenta Nafiu Baba Ahmad ya sanya wa hannu.
A cikin sanarwar, majalisar ta nuna bakin ciki matuka kan abin da ta bayyana a matsayin mummunan kisan gilla, tana cewa harin da aka kai a kauyen Woro, inda mata da yara suka rasa rayukansu tare da kona gidaje, ya nuna tabarbarewar tsaron Nijeriya cikin yanayi mai firgitarwa.
Ta jaddada cewa abin da ya faru a Kwara wani bangare ne na irin tashin hankalin da aka samu a baya-bayan nan a jihohin Katsina, Kaduna, Zamfara da Borno, lamarin da ke nuna raguwar mutunta rayuwar dan Adam a fadin kasar.
Majalisar ta yi karin haske cewa kare rayuwar dan Adam ka’ida ce da ba ta da sassauci a Musulunci, tare da cewa kashe fararen hula ba tare da la’akari da addini ko kabila ba na daga cikin manyan laifuffuka da ke saba wa addini da kuma tunanin bil’adama.
Ta kuma yi Allah wadai da hare-haren da ake kai wa Musulmi da Kiristoci baki daya, ko ta hanyar ta’addanci, fashi da makami ko rikicin kabilanci, tana cewa ci gaba da faruwar irin wadannan laifuka duk da alkawuran da ake ta bayarwa na nuna gazawa a bangaren shugabanci da tsarin tsaron kasa.
Majalisar ta amince da kokarin jami’an tsaro, amma ta bukaci masu rike da mukaman gwamnati su mayar da hankali kan babban nauyinsu na kare rayuka da dukiyoyi, tana gargadin cewa shugabanci amana ce, kuma idan aka gaza kare jama’a, alhaki na bin hakan bisa koyarwar Musulunci da ka’idojin dimokuradiyya.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa majalisar ta mika ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa a Woro da sauran sassan kasar, tare da yin addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata, sannan ta yi maraba da sakin wasu mutanen da aka yi garkuwa da su a Kurmin Wali.
Haka kuma ta yi kira ga hukumomi su kara kaimi wajen kubutar da sauran da kuma tarwatsa kungiyoyin aikata laifuka, tare da yin kira ga dukkan matakai na gwamnati, jami’an tsaro, shugabannin al’umma da ‘yan kasa da su hada kai domin dakile zubar da jini da rashin doka da oda a Najeriya.













































