Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya shiga zanga-zangar da ta mamaye Majalisar Dokoki a birnin Abuja a ranar Litinin, kan batun tura sakamakon zaɓe ta hanyar na’urar lantarki.
Zanga-zangar ta biyo bayan amincewar Majalisar Dattawa da kudirin gyaran Dokar Zaɓe ta 2022 a shekarar 2026 a karatu na uku, inda ‘yan majalisar suka cire kalmar tura sakamakon zaɓe ta hanyar na’urar lantarki kai tsaye daga kudirin dokar.
Ko da yake Majalisar Dattawa ta fitar da bayanai daban-daban domin yin karin bayani kan rahotannin da ke cewa ta ƙi amincewa da tura sakamakon zaɓe ta hanyar na’urar lantarki, masu zanga-zangar sun nace cewa dole ne ‘yan majalisar su sake saka batun tura sakamakon zaɓe ta hanyar na’urar lantarki kai tsaye a cikin kudirin dokar.
Peter Obi, wanda a yanzu mamba ne na jam’iyyar ADC, yana daga cikin masu zanga-zangar da suka hallara a ƙofar Majalisar Dokoki.
Ya jaddada bukatar Majalisar Dattawa ta dauki matakan hana matsalolin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta fuskanta a shekarar 2023, tare da sanya tura sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki kai tsaye a matsayin wajibi a doka.
Mambobin kungiyoyin fararen hula, wasu ‘yan jam’iyyar ADC ta adawa, da kuma wasu kungiyoyin mata suna daga cikin masu halartar zanga-zangar.
Masu zanga-zangar sun fara tattakinsu daga sakatariyar gwamnatn tarayya, suna nufar ƙofar Majalisar Dokoki, inda aka ga jami’an tsaro da yawa daga rundunar ‘yan sanda ta Najeriya, sojojin Najeriya, da jami’an tsaron fararen hula suna tsare wurin, tare da toshe hanyar shiga Majalisar Dokoki.
Yayin da aka bayyana cewa zanga-zangar za ta gudana ne a bakin ƙofar majalisar ba tare da shiga cikinta ba.













































