Hedkwatar tsaron kasar nan ta yi Allah-wadai da ikirarin cewa manyan hafsoshin soji sun ba da gudummawar kudi domin a sako Birgediya janar Mahrazu Tsiga, wanda aka yi garkuwa da shi tsawon kwanaki 56.
Daraktan yada labarai na tsaro Manjo janar Tukur Gusau, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce ikirarin da Birgediya mai ritaya janar Ismaila Abdullahi ya yi ya sabawa kokarin sojoji.
Gusau ya ce, labarin ya nuna a fili karara kokarin da sojojin Operation Fansan Yamma suka yi ta hanyar gudanar da aikin ceto Janar Tsiga bai yi tasiri ba.
Ya ce babban jami’in a cikin sakon ya mika godiyarsa ga sauran manyan hafsoshi da fararen hula bisa gudunmawar da suka bayar wajen ceto tsohon Darakta Janar na masu kula da yi wa kasa hidima (NYSC).
A cewar mai magana da yawun rundunar, yana iya zama kamar rashin amfani a yi hulda da wadanda ke sukar sojoji akai-akai, musamman wadanda suka ci gajiyar aikin soja.
Ya ce ya zama wajibi a fayyace irin namijin kokarin da sojojin suka yi wanda ya taimaka wajen sakin Janar Tsiga.
Karanta: Nuhu Ribadu ya mika Janar Tsiga, Ambasada Yohanna da wasu 17 da aka yi garkuwa da su ha iyalansu
Gusau ya kara da cewa, a ranar 8 ga watan Fabreru, sojoji sun kara kaimi wajen farautar masu garkuwa da mutane tare da kai hare-hare da asuba a Yankuzo da Gidan Dankaka dake karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara inda sarkin ‘yan ta’addan Ado Aliero ya yi garkuwa da su.
Ya kara da cewa harin da jiragen sama suka kai a Dutsen Dunya, wanda ake zargin tungar ‘yan ta’adda ne inda ake tsare da Janar Tsiga, ya tarwatsa ‘yan ta’addan, wanda ya kai ga tserewar da dama daga cikin wadanda aka kama.
A cewarsa, janar Tsiga ya kasa tserewa saboda rashin lafiya.
Kakakin rundunar tsaron ya bayyana cewa, tun bayan sace Tsiga, sojojin sun ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu na sama da na kasa, wanda ya kara da cewa, sun ci gaba da matsa lamba kan wadanda suka sace shi.
A cewarsa, ya dace a gane irin sadaukarwar da wadannan sojojin da suka yi aiki dare da rana suka bayar, wadanda galibi suna cikin hatsari ga rayuwarsu wajen ceton sa. (NAN)













































