Remi Tinubu ta ba da gudummawar Naira Biliyan 1 don yaki da cutar daji

Remi Tinubu with Iziaq Salako 750x430

Mai dakin shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta ba da gudummawar Naira biliyan 1 ga asusun kula da cutar daji na kasa domin tallafawa yaki da cutar sankarar mahaifa.

Uwargidan shugaban kasar, yayin da take karbar tawagar kwamitin yaki da cutar kansar mahaifa ta kasa karkashin jagorancin karamin ministan lafiya Iziaq Salako, ta ce babu bukatar jin kunyar neman taimako ga masu fama da cutar.

Salako ya bayyana jin dadinsa ga tallafin da uwargidan shugaban kasar ta bayar, wanda ya ce ya ba da damar yin allurar rigakafin ga yara mata miliyan 12 da ke tsakanin shekaru 9 zuwa 13 a cikin watanni tara na farko na rigakafin cutar papillomavirus (HPV).

Ya ce ma’aikatar lafiya na fatan yiwa ‘yan mata miliyan shida rigakafin a wannan shekara.

Shugaban kwamitin da ke yaki da cutar kansar mahaifa Isaac Adewole, ya yabawa Remi Tinubu kan rashin nuna ra’ayin siyasa ta hanyar tallafa wa wajen bada allurar rigakafin cutar ta HPV a cikin shirin rigakafi na yau da kullun.

Ya ce tare da goyon bayanta, za a iya cimma burin yiwa ‘yan mata miliyan 8 rigakafin a kowace shekara, ta yadda za a kawar da kansar mahaifa nan da shekarar 2030.

Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Walter Mulombo, ya yi kira ga uwargidan shugaban kasar da ta jagoranci gangamin, inda ya ce kowane yaro da mace na da ‘yancin rayuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here