Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana kiran da gwamnatin Kano ta yi na a kama shi kan zargin kafa wata runduna a matsayin abu maras tushe, ganganci kuma alamar rashin iya aiki.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Edwin Olofu, Ganduje ya ce wannan kira da aka yi na kama shi abin ganganci ne, babu tushe, kuma ya nuna rashin ƙwarewar gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya ce irin wannan mataki na nuna kin cika nauyin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman ganin yadda gwamnatin ta kasa magance matsalar tsaro a jihar.
Ganduje ya ce maimakon gwamnan ya maida hankali kan hare-haren da ke addabar kananan hukumomin Bagwai, Shanono, Tsanyawa da sauran yankuna, sai ya tsunduma cikin neman wanda zai ɗauki alhakin gazawarsa, alhali bai kai wa waɗanda abin ya shafa ziyara ko nuna tausayawa ba.
Labari mai alaƙa: Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta nemi a kama tsohon gwamna Abdullahi Ganduje
Ya ƙara da cewa shi ba a taɓa danganta shi da tashin hankali ko wani abu da zai kawo tangarda ga zaman lafiya a Kano ba, yayin da a lokacin mulkinsa jihar ta kasance cikin kwanciyar hankali na tsawon shekaru takwas, abin da ya sa ake yaba masa a matakin ƙasa.
Ganduje ya jaddada cewa gwamna Yusuf ya kamata ya maida hankali kan nauyin da kundin tsarin mulki ya dora masa na kare rayuka da dukiyoyin mazauna Kano, maimakon shiga wasan siyasa da watsar da zarge-zarge marasa tushe.
Ya ce shugabanci gaskiya yana nufin ɗaukar mataki mai ma’ana, nuna alhaki da tausayawa, ba wai yin taron manema labarai da fitar da bayanai marasa amfani ba.












































