
Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Majalisar ministocin kasar Iran ta kira wani taron gaggawa na biyu cikin kasa da sa’o’i 24 bayan tabbatar da mutuwar shugaban kasar Ebrahim Raisi.
Kafofin yada labaran cikin gida sun rawaito cewa a ranar Litinin mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad Mokhber ya riga ya jagoranci wani taro a yammacin Lahadi bayan da jirgin mai saukar ungulu ya bace tare da mutane tara a cikin jirgin a yankin arewa maso yammacin Iran.
Karin labari: Kotu tayi watsi da bukatar Tukur Mamu kan dauke shi daga hannun DSS zuwa gidan yarin Kuje
Rahoton ya bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian shi ma ya mutu a hadarin jirgin sama mai saukar ungulu.
Raisi da Amirabdollahian suna dawowa ne daga ganawar da suka yi da shugaban kasar Azarbaijan, Ilham Aliyev, lokacin da jirginsu ya bace daga radar a yammacin Lahadi.
Karin labari: “Ma’aikata za su zauna a gida maimakon karbar Naira Dubu 48,000” – NLC
Bisa ga ka’idar, tare da mutuwar Raisi, Mokhber ya kamata ya karbi mulki, yana jiran amincewa daga jagoran koli Ayatullah Ali Khamenei.
Daga nan sai a gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 50.