NDLEA ta tarwatsa dandalin shaye-shaye tare da kama mutane 18 a Kano

NDLEA 1
NDLEA 1

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta ce ta kama wasu mutane 18 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi daban-daban a jihar.

Sadiq Muhammad-Maigatari shi ne mai magana da yawun hukumar ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Juma’ar nan.

Muhammad-Maigatari ya ruwaito kwamandan hukumar na jihar, Abubakar Idris-Ahmad, ya bayyana cewa an kama su ne a wani samame da suka kai a wani mataki na yaki da miyagun kwayoyi a jihar.

“A ranar 30 ga watan Janairu, hukumar ta tarwatsa wasu fitattun wuraren shan miyagun kwayoyi da ke Unguwar Fagge, Kwarin Kaya, Kofar Wambai, da Kofar Mata”.

“An kai samame a Kwarin Kaya musamman, domin wasu da ake zargin sun yi yunkurin yi wa jami’anmu barazana, sai dai duk da wannan tsoratarwa, NDLEA ta ci gaba da jajircewa a kan aikinta, tare da tabbatar da cewa an gudanar da aikin ba tare da wata matsala ba,” in ji shi.

Ya ce hukumar ta samu nasarar kwato wasu haramtattun abubuwa kamar su tabar wiwi da da makaman da aka kera a cikin gida”.

Ya kuma jaddada kudirin hukumar na kakkabe kungiyoyin ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma kawar da shan miyagun kwayoyi a jihar.

“Hukumar ta himmatu wajen gurfanar da duk wadanda ke da hannu a laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi, kuma za ta ci gaba da gudanar da ayyuka da nufin kare al’umma daga hadurran da ke tattare da shaye-shayen miyagun kwayoyi,” inji shi (NAN).

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here