Karuwar Rashin Tsaro: Majalisar Shari’a ta bukaci gwamnati ta dauki mataki gaggawa

Bandits. Photo Credit ZAgazola 750x430 (1)

Majalisar Koli ta Shari’a a Najeriya (SCSN) ta bayyana fushinta kan ta’azzar rashin tsaro a fadin kasar, inda ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakai da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyi.

A cikin sanarwar da sakataren majalisar, Nafi’u Baba Ahmad ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce ‘yan Najeriya na ci gaba da fuskantar rahoton kisan kai, sace-sace, hare-haren ‘yan ta’adda, barayi da sauran laifukan zubar da jini a kullum duk da alkawuran da jami’an gwamnati ke ci gaba da yi.

Majalisar ta bayyana halin tsaron yanzu a matsayin mai tayar da hankali, inda ta bayyan cewa a kwanan nan an yi sace-sace da kai hare-hare da yawa a jihohin Borno, Oyo, Niger da Zamfara, tare da sace Janar din Soja mai ritaya da matarsa a Jihar Katsina.

A cewar Majalisar, al’amuran sun nuna yadda al’ummomin da suka dade suna fama da rashin tsaro ke cikin hadari.

Ta ce hare-haren da aka ruwaito bangare ne kawai na munanan abubuwan da ‘yan Najeriya ke fuskanta kullum, da dama daga cikinsu ba a ruwaito su ba.

Majalisar ta ambaci rahotanni daga kungiyoyin sa ido kan tsaro da kare hakkin dan adam da ke nuna dubban ‘yan Najeriya an kashe su, an sace su ko aka raba su da gidajensu a watannin da suka gabata.

“A bayan kowane lamba akwai labarin dan adam, rayuwar da aka kashe ko ta rushe, iyali da ya shiga cikin bakin-ciki, da al’umma da aka tilasta musu rayuwa cikin tsoro, rashin tabbas, da rashin tsaro,” in ji sanarwar.

Majalisar ta yi koka cewa kira-kiran da ‘yan kasa masu kishin kasa, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, kungiyoyin jama’a da sauran masu ruwa da tsaki suke yi na bukatar gwamnati ta shiga tsakani bai haifar da ci gaba mai yawa ba.

“‘Yan Najeriya sun gaji da jawabi, alkawari, ta’aziyya, kwamitoci, da maganganun gwamnati da ba su da aiki ko sakamako, abin da kasa ke bukata yanzu shi ne mataki mai karfi da sakamako da za a iya aunawa,” in ji ta.

SCSN ta jaddada cewa tsaro ba alfarma ba ne, hakki ne na gwamnati a kundin tsarin mulki, inda ta gargadi cewa babu gwamnati da za ta iya cewa ta yi nasara yayin da manyan sassan kasar ke cikin hadarin ‘yan laifi.

“Lokaci ya yi da masu rike da madafun iko ko dai su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ko kuma su mika mulki ga wadanda za su iya,” in ji Majalisar.

Yayin da suke kalubalantar gwamnati kan yadda take tafiyar da tsaro, Majalisar ta yaba wa sojoji da sauran jami’an tsaro bisa sadaukarwarsu da kudurin su na kare kasa a cikin yanayi mai wahala.

“Don haka kalubalenmu ba ga jami’an tsaronmu masu kishin kasa ba ne wadanda ke ci gaba da sadaukar da kansu wajen kare kasar mu,” in ji sanarwar.

Majalisar ta kuma bukaci a kara yin aiki cikin gaskiya da bayyana yadda ake sarrafa kudaden da aka ware wa fannin tsaro, inda ta lura da cewa an kashe tiriliyoyin Naira kan tsaro, tattara bayanai, ayyukan soja, kayan aikin tsaro da dabaru a tsawon shekaru.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here